Kundin Tsarin Mulkin Masarautar Kano

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Kundin Tsarin Mulki


Gabatarwa

Kudin tsarin mulkin masarautar Kano, kundi ne da fitattaccen malami Muhammadu Mugili ya rubuta wa sarkin Kano Muhammadu Rumfa tun sama da shekaru ɗari shida da suka shuɗe.

Littafi ne da yake ɗauke da wasu ƙai’dodi da dabaru da shawarwarin gudanar da sarauta da kuma muƙamai da sauran abubuwa da wannan malami ya rubata wa sarkin domin ya samu cikakkiyar damar gudanar da mulkinsa a bisa tafarkin shari’ar Musulunci.

Wasu jama’a da dama suna ganin cewa, wannan kundin tsarin mulki kusan shi ne maɓuɓɓugar dabarun gudanar da mulki a fakaice da Turawan Mulkin Mallaka suka yi amfani da shi da farko a Arewacin Najeriya, daga baya a duk faɗin Najeriya, daga ƙarshe kuma a duk ƙasashen da suka mulka a yankin Afirka ta Yamma.

Wazirin Kano Abubakar (1972), ya labarta cewa, a lokacin da Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya hau karagar sarautar Kano, ya waiwaci tsare-tsare da kuma salon sarautar Hausawa domin samun cikakken goyon bayan Kanawa wajen gudanar da mulki. Kuma sannu a hankali waɗannan tsare-tsare su ake gani a cibiyar Daular Usmaniyya, kama-kama har lokacin da Turawa suka ci Ƙasar Hausa da yaƙi, suka fara tsarin Hukumar Gargajiya, sannan suka faɗaɗa sauran lardunan Arewa har zuwa dukkan ƙasashen da suka mulka a Afirka ta Yamma kamar yadda fitaccen masanin tarihin Afirka ta Yamma, Farfesa Boahen (1986), ya wallafa a Littafinsa.


Ƙofar Gidan Sarkin Kano; Gidan Rumfa

Abin Da Ke Cikin Kundi

Bayan haka, Allah Ya datar da kai da jin trosonSa, Ya tsare ka daga fizgar son zuciya. Haƙiƙa sarauta halifanci ce daga Allah sannan kuma wakiltar Manzon Allah (SAW) ce. Ya girman falalarta! Ya nauyin maɗaukinta!

Idan sarki ya yi adalci, tsoron Allah zai yanka shi ta hanyar tsinke jijiyoyin son zuciya. Idan kuma ya yi zalunci son zuciya zai yanka shi ta hanyar tsinke jijiyoyin tsoron Allah.

Na gargaɗe ka da jin tsoron Allah (Kowane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijarorinku kawai ne a Ranar Ƙiyama. To, wanda aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne ya tsira. Kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face jin daɗin ruɗi. Alƙur’ani, 3:185).

Babi Na Farko

Babi ne da ya yi magana a cikin kyautata niyya ga sarki a cikin dukkan al’amuran sarautarsa. Cewa ya ƙudurci neman yardar Allah da wannan sarauta tasa ba duniya ba. Malam ya ce:

Dole ne a kan sarki ya kyautata niyya a cikin sarauta. Ya nemi taimakon Allah a cikin dukkan al’amuransa. Ya ƙudurci samun yardar Allah da ita ta hanyar gyara al’amuran da suka shafi addini da duniya na bayin Allah.

Ya sani cewa, haƙiƙa Allah bai jiɓintar da shi a kansu domin kawai ya zama shugabansu ba, a’a, sai domin ya daidaita musu addininsu da duniyarsu. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Babi Na Biyu

Daga cikin abubuwan da suke zama dole a kan sarki akwai kyautata kwarjininsa a majalisa ta hanyar bayyana son alheri da ma’abotansa da kuma ƙin sharri da ma’abotansa.

Cikin abin da ya shafi tufafi, to ya yi sutura da abin da yake halastacce ne ga maza (Wato abin da aka sani na suturar maza), wanda bai yi kama da na mata ba. Kar ya ɓarnatar da dukiyar talakawa a wajen ado. Kar ya yi ado da zinare, azurfa da kuma alharini.

Dole ya zauna a cikin nutsuwa ba tare da wasa ba, kuma sannan kar ya zama mai ƙyalƙyala dariya. Ya zama mai runtse ganinsa, mai karɓar ra’ayi bisa gaskiya. Ya zama mai ƙin abubuwan ƙi kamar irin su ƙarya, saɓa alƙawari da kuma gafala a cikin umarninsa da haninsa.

Mutanen da ke zagaye da shi su zama mutanen kirki ne da kuma malamai masu son alheri, da masu tsoron Allah da masu gyara da masu gudun duniya. Duk su zama su za su kusance shi. Sannan kuma ya nisanci jahilai da fajirai.

Ya zamo jajirtacce a cikin rarraba dukiyar al’umma da kuma tsare sarautarsa a kan-kansa da kuma iyalansa. Kar ya zamo bawan riga (Duk wanda ya ga dama ya ya ɗauka ya saka), kar kuma ya zama doki (Kowa ya so, sai ya hau kansa) kuma kar ya zama shimfiɗa (Kowa ya zo ya hau kanta ya huta) kuma kar ya zama gurin zama (Duk shimfiɗar da ake so sai a shimfiɗa a kai a zauna). Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Babi Na Uku

Babi ne da ya yi magana a game da tsara masarauta ta hanyar rarraba ayyuka ga jami’an da za su dafawa sarki wajen gudanar da sarautarsa a dukkan faɗin masarautar. An lissafa muƙamai ishirin da biyar daki-daki kuma kowane ɗaya da irin ayyukan da suka kama ce shi tare kuma da siffofi ko siffar wanda ya kamata a naɗa a kan kowane muƙami. Malam ya ce:

Babi na huɗu cikin abubuwan da suka zama dole a kansa game da tsara masarautarsa ta yadda gyaranta zai zama abu mai yiwuwa a gare shi. Saboda zamowarsa mai kula da kowa sannan kuma abin tambaya ne shi (A gaban Allah) game da su.

Wannan kuwa (Kula da dukkan masarauta) ba abu ne mai yiwuwa a gare shi shi kaɗai ba, dole sai da wakilci. Saboda haka zai samar da muƙamai kamar haka:

  1. Wazirai: Wazirai su ne masu taimaka masa a wajen kula da harkokin siyasa a dukkan faɗin masarautarsa (Su ne irin su galadima, wali, chiroma da sauransu). Su zamo marasa tsoron kowa sai Allah kaɗai.
  2. Shugabanni: Su ne masu jagorantar garuruwan da suke nesa da shi. Masu tara masa jama’a a duk lokacin da yake buƙata (Waɗannan su ne hakimai, digatai da masu unguwanni).
  3. Alƙalai: Su ne masu raba rigingimu (Wato masu gudanar da shari’o’i) a tsakanin jama’a. Su zamo masu tsoron Allah.
  4. Jami’an Tsaro: Su ne ‘yan hisba masu umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani ga aikata mummunan aiki. Masu kula da kai-kawon al’amuran birni da sauran abubuwan da suka shafi al’umma (Kamar tarurrukan bukukuwa, ibada, zamantakewar ma’aurata da sauransu, abubuwan da suke buƙatar sasanto ba shari’a ba).  Kuma masu gyara abin da ya lalace (Na daga tarbiyya da sauransu).
  5. Dogarawa: Su ne masu taimaka masa wajen kula da hukunce-hukunce (Su ne masu kamo duk wanda ya yi laifi tare kuma da ladabtar da shi).
  6. Fadawa: Su ne masu zama tare da sarki; masu aiwatar da buƙatunsa domin kar ya buƙatu da wasun su.
  7. Mashawarta: Su ne mutane masu hankali, waɗanda za su riƙa yi masa nuni a cikin abubuwa kafin abin ya kai ga jama’a (Siffarsu ita ce hankali. Duk kuwa mutum mai hankali za a same shi da hangen nesa, taka tsan-tsan da sauransu).
  8. Ma’aikatan Zakka: Su amintattun mutane ne da za su riƙa karɓo dukiya suna sarrafa ta bisa dacewa (Siffarsu ita ce amana).
  9. Marubuta: Su ne waɗanda taskace dukkan abubuwa ya hau kansu.
  10. ‘Yan Aike: Su ne masu kai-kawo a tsakanin garuruwan Musulmi.
  11. ‘Yan Leƙen Asiri: Su ne suke zama idon sarki a garuruwan maƙiya (Wato jami’an tsaron farin kaya kenan).
  12. Masu Gadi: Su ne masu tsaron sarki da rana.
  13.  Masu tsaron sarki da daddare.
  14. Malamai: Mutane ne masu zuzzurfan sani ababen dogaro a fagen ilimi da kuma tsoron Allah. Aikin su shi ne shiryatar da sarki a cikin dukkan lamuransa.
  15. Masu Ceto: Mutane ne da suke nema wa mai laifi rangwame game da horon da za a yi masa. Amma banda waɗanda aka yankewa haddi da kuma wanda ya ci haƙƙin wani (Biyun ƙarshen nan kam dole a zartar da hukunci, babu sassauci).
  16. Masu Tsare-Tsare: Su ne mutanen da suke yin gyara domin Allah.
  17.  Ma’aikatan Kuɗi: Su ne masu karɓo haƙƙin Allah kamar zakka da dukiyar ƙasa.
  18. Ɗakin Ajiya: Ɗaki ne wadatacce wanda za a riƙa ajiye kayan abincin sarki, abubuwan sha da sauransu.
  19. Doki: A tanadi ƙarfafan dawakai a taskar dukiyar ƙasa domin hawan sarki zuwa kai harin jihadi wasu biranen komai nisansu (Daga cikin irin waɗannan dawakai akwai wanɗanda ake tanada domin sarki ya fece daga filin daga idan rana ta ɓaci. Saboda haka irin waɗannan dawakai akan same su da ƙarfi, gudu da kuma iya tsallake kwazazzabai da sauransu).
  20. Guzuri: Dukiya ce da ake tanada musamman a taskar dukiyar ƙasa domin ɗawainiyar marasa hali a lokacin tafiya jihadi da sauran abubuwa.
  21. Dakaru: Gwarazan mutane ne sannan kuma jarumai, waɗanda suke kewaye da sarki a kodawane lokaci domin shirin ko-ta-kwana.
  22. Kayan Yaƙi: A tanadi nagartattun kayan yaƙi kamar irin su kwari da baka, masu, garkuwa, sulke da sauransu masu tarin yawa.
  23. Likitoci: A samu mutane yardaddu, waɗanda za su riƙa bai wa mutane magunguna saboda kar su mutanen su  buƙatu ya zuwa garin da ba nasu ba (Kar su buƙatu da zuwa ƙasashen waje domin kiwon lafiya).
  24. Shugabannin Rundunoni: Su ne mutanen da suke jagorantar rundunonin yaƙi (Misali, sarkin baka da yake jagoratar maharba a filin yaƙi). Waɗannan su suke wakiltar sarki a cikin lamarin yaƙi. Ayyukan su sun haɗa da shirya runduna, kare hasken Musulunci da sauransu.
  25. Masana Yaƙi: Mutane ne waɗanda ra’ayinsu yake yaye baƙin ciki, saboda tabbas shi yaƙi ɗan zamba ne amma ba yawa ko sauri ba. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Babi Na Huɗu

Wannan babi ne da ya yi magana game da zaman jiran ko-ta-kwana a lokacin da ake zaune a gida ko a halin tafiya a yayin da yanayi ya canja daga aminci zuwa tsoron kawo hari daga abokan gaba da kuma irin matakan da suka kamata sarki ya ɗauka. Malam ya ce:

Lazimtar taka-tsan-tsan a halin zaman gida ko kuma na tafiya ta hanyar bayyanar da ƙarfi da kuma juriya (Juriya a nan na nufin sarki ya jure wa dukkan irin firgici, razani da tsoron da yake ransa ya danne shi kar ya sake ya bayyana a fili mabiyansa su gane. Hakan zai karya musu gaba) a yayin canjawar yanayi zuwa na tsoro.

Ya zama mai bayyana gudun-duniya a cikin abin da ya shafi matarsa da ɗansa saboda kar su hana shi aikata adalci (Lalle ne daga matanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Alƙur’ani, 64:14).

Ya zama mai bayyana kwaɗayinsa wajen rashin ɗaukar ɓangare da kuma daidaito. Sannan ya zama mai son fita zuwa jihadi. Ya zama mai ƙin zama a cikin gida. Wannan za ta ɗaukaka kimarsa a idon abokan gaba.

Zaman sarki a cinkin gidansa ga barin jama’arsa, shi ne tushen kowace fitina da kuma ɓarna. Shi mulki da takobi ake yin sa ba da sanyin jiki ba. Abin nufi, ba zai yiwu da faɗin cewa da sannu zan kai musu hari, da sannu zan aikata ba. Anya kuwa zai yiwu a kawar da tsoro a cikin firgici? Tabbas duk wanda ya tsoratar da kai, to kar ka miƙa masa wuya sai ka razana shi kuma ba tare da ka yaƙe shi ba ko ka nemi sasantawa da shi ba (Kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zuwa ga sulhi alhali kuwa ku ne mafi ɗaukaka, kuma Allah na tare da ku. Alƙur’ani, 47:35).

Dole ya zama mai taka-tsan-tsan a cikin abincinsa da abin shansa da makwancinsa. Kar ya jiɓintar da kowa sai makusanta kuma masoyansa.

Kar ya zauna a majalisa ba tare da jaruman mayaƙan ƙasa da kuma mahaya dawaki ba. Kuma su zama amintattu sannan kuma jarumai. Lokacin zaman ɗar-ɗar ba ɗaya yake da lokacin zaman lafiya da kwanciyar hankali ba.

Ya zama mai ɓoye sirrinsa. Kar ya riƙa yarda da zantukan annamimai ko da sun haura saba’in. Su kuwa masu zato (Abokan gaba), kar ya yaudaru da bayyanar ‘yan aikensu, kyautar girmamawa tana amintar da su. Gwarazan cikinsu kuma a basu babbar kyauta (Kuma lalle ni, mai aikawa ce zuwa gare su da kyauta, sa'an nan mai dubawa ce da me manzannin za su komo. Alƙur’ani, 27:35).

A cikin abin da ya shafi garuruwan da ke kusa da maƙiya, ya rushe dukkan garuruwan da ba zai yiwu amintattunsa su zauna a ciki ba. Saboda kar (Garuruwan) su tanadar masa maƙiya. Ya nisanci igiya saboda gudun cizon maciji. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Babai Na Biyar

Babi ne da ya yi magana a kan wasu al’amuran rayuwa masu rikitarwa waɗanda suka zama dole sarki ya warware su ta cikin hikima, bisa amana da kuma adalci. Malam ya ce:

Babi na biyar, cikin abubuwan da suka zama dole a warware su bisa adalci da amana daga cikin abubuwan da suke shige wa talakawansa duhu kamar lamarin waɗanda aka tsare dukiyarsu. Marayan da aka hana shi sarrafa dukiyarsa to mai kula da shi ne zai ɗauki ɗawainiyar rayuwarsa.

Haka nan a saka tsantseni da lura wajen warware al’amuran da suka shafi ɓoyayye (Mutumin da ya yi tafiya sannan kuma ya ɗauki dogon lokaci babu labari), gadon matattu, alamuran dukiyar al’umma da kuma albashin ma’aikata. Kar a saka cutarwa da kwaɗayi a ciki. Kamar abin da ya shafi albashin ma’aikatan kuɗi na daga abin da yake ƙaruwa a gare su na kuɗi.

Duk wanda yankewa ta bayyana a gare shi (Wato duk wanda ya yanke wa wani kuɗi; wand aka iya zama albashi ko waninsa, kuma aka gane) to a tsawatar masa. Wanda kuma ya yi zalunci a cire shi. Wanda kuma ake yin ƙorafi a kansa a canja shi idan za a samu wanda zai canje shi. idan kuma ba haka ba, to sarki ya rasa amintattu.

Duk wanda kuɗi suka ƙaru a kan abin da ya dace a biya shi, to a karɓe (Ƙarin) a saka a shi a cikin gyaran al’amuran Musulmi. Idan kuma aka yi kokwanto a kai, to a rantsar da shi (Wato idan ya ce nasa ne sai a saka shi ya rantse a kan haka). Ya (Sarki) kasance a gare su (Talakawanka) kamar mai kiwon dabbobi a tsakanin mafarautan zakuna (Wato zakunan da suke farautar abinci). Dukkan ɓarna tana tare da gurɓataccen albashi.  

Aikin ma’aikatanka aikinka ne. idan ya kyautatu, ladan naku ne baki ɗaya. idan ya munana, horon yana kanku.

Game da masu burin aikata ɓarna, haƙiƙa buri yana tabbata da samuwar alamomi. Babu makawa wajen warware shi idan aka tabbatar da shi. Idan kuma ba haka ba, to sai a hukunta shi bisa dacewa gwargwadon kusancinsa da nisansa. Sannan kuma a toshe kafar aikata laifin.

Game da abin da ya shafi al’amuran abokan gaba kuwa, to babu makawa wajen warware shi ta hanyar leƙen asirin amintattu. Haƙiƙa jahilci makanta ce. Mutum ɗaya mai ido zai iya rinjayar makafi dubu. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne ya wofintar da talakawansa. Zargin masu zargi da yabon masu yabo, dole a warware su ta hanyar amintattu.

Babi Na Shida

Abubuwan da suka zamar masa dole ta fuskacin adalci da kuma kyautatawa. Abin da ake nufi da adalci shi ne a bai wa mai haƙƙi haƙƙinsa. Duk ɗaya ne zamowar haƙƙin nasa na ƙashin kansa da kuma na talakansa. Duk wanda baya bai wa talakawansa haƙƙin da ya shafe su to wannan ba adali ba ne.

Ita kuwa kyautatawa, ita ce ya fifita da kansa. Abin nufi shi ne ya ƙarawa duk wanda ya yi nufin ya kyautatawa; ƙari daga cikin abin yake shi ne haƙƙinsa, amma ba da rabon waninsa ba. Duk wanda ya kasance yana kyautata wa mutane ta hanyar basu fiye da abin da suka cancanta daga cikin dukiyar da dukkan jama’a suka yi tarayya a cikinta ba tare da yardarsu ba, to bai zama mai kyautatawa ba, a maimakon haka ma shi azzalumi ne. Saboda abin da ya yi kyautatawar da shi bai keɓanta da shi ba a shari’ance. Ka fahimci wannan lamarin, kar ka yi burinsa.

Adalci ne daidaita tsakanin mutane masu rigima a cikin dukkan lamuransu. Kuma kar ya karɓi sheda sai ga wanda ya kasance adali kuma yardajje; wanda babu tuhuma a kansa. Idan kuma adalcin ya wuyata, to ya lura da kwatankwacinsa ta fuskacin gaskiya tare da bayyanarta wato sanuwa a kan gaskiya. Kar ya wadatu da guda biyu, kuma ya zama akwai siyasa da lura a cikin lamarin. Sannan dole ya yi wa wanda ake ƙara bayanin dalilan da suka saka aka yi ƙararsa, sannan kuma ya kafa masa hujja idan yana nufin hukunta shi; dole ya yi masa cikakkiyar warwara game da dalilan da suka tabbatar da hukuncin a kansa. Sannan ya kafa masa hujja da cewa: “Ko kana da sauran hujja?” Idan ya ce akwai, sai ya sake yi masa warwara. Idan kuma ya ce babu, sai a hukunta shi. Kuma hukuncin ya zamo bayan an tuntuɓi malamai. Baya halasta ya hukunta koma menene sai bisa abin da ya bayyana a mazahabar limaminsa. Tabbas hukunci da wanin abin da aka saba da shi zalunci ne, sannan kuma taɓewa ce, kuma dole a warware wannan hukunci ta kowane hali.

Ikirarin manyan laifuffuka yana keɓantuwa da nau’ukan siyasa. Manyan laifuffuka kuwa su ne kamar irin su sata da kisan kai. Duk wanda aka ce ya yi sata ba tare da hujja ba, to ba zai kuɓuta daga ɗayan abubuwa uku ba:

Na Farko: Idan ya kasance ya nisanta daga abin da aka dangata shi da shi, to a yi watsi da maganar sannan kuma a ladabtar da wanda ya faɗi maganar idan wanda aka faɗi maganar a kansa ya kasance mutumin kirki ne.

Na Biyu: Idan ya kasance ya kusanci abin da aka danganta shi da shi, to dole a kama shi a tsare, a hukunta shi da bulala gwargwadon laifinsa tare da jin tsoron Allah a cikin lamarin. Wasu lokutan zai iya kuɓuta ko laifin ya tabbata a kansa, to sai ya yi rantsuwa kamar yadda aka saba. Saboda sanuwa da ya yi da kuma yawan maimaituwar maganar a kansa, hujja ce a gurin wanda ya faɗi maganar a bisa abin da aka saba da shi. Duk wanda aka yawaita yi masa horo har ya sanu da wannan, to a tsare shi har sai tubarsa ta bayyana ko kuma a aika shi ƙabari.

Na Uku: Idan ya kasance miskili ne shi, sai a tsare shi har sai alƙali ya fahimci irin halinsa, sannan a yi masa hukuncin da ya dace. Idan kuma ba haka ba, to a sake shi. Hakan zai zama siyasa tare kuma da horo da bincike; gwargwadon yadda saka ido da shaida za su iya hukunta shi. Dukkan waɗannan a yi su bisa tsoron Allah ba bisa son zuciya ba. Mutane basu taru sun zama ɗaya ba.

Duk wanda aka ce ya yi kisan kai, to dole a kama shi a tsare a matakin farko. Idan kuma laifin ya tabbata a kansa sai a hukunta shi. idan kuma ba haka ba, to sai a lura da duk wanda yake cuɗanya da su ta fuskacin nisa da kuma kusanci. Idan ya kusanta (Da laifin), to sai a tsawaita ɗaurin. Idan kuma ya nisanta sai a gaggauta sakinsa.

Dole ne babban sarki ya riƙa zama (A majalisarsa) a kowace rana domin dukkan talakawansa su riƙa samun zuwa gare shi. Ma’aikatansa da sauran masu riƙe da sarautu ba su isar masa ba. Saboda ƙorafin waɗanda yake mulka zai iya kasancewa a kansu ne. Saboda haka dole ya gargaɗe su. Idan kuma ba haka ba, to ya zama kamar kwando ga kayan cikinsa ko kuma mariƙin ƙahon saniyar tatsa. Haƙiƙa an cire nagartattun ma’aikata masu wakilci saboda koke. Wannan kuma shi ya fi kusa da jin tsoron Allah. Mafi girman bala’i a gare shi, shi ne a shiga tsakaninsa da talakawansa.

Kai sake waiwatar wannan shafi domin ƙarashen bayanin da ke cikin wannan kundin tsarin mulki mai daɗaɗɗen tarihi.

Manazarta:


Al-Illori A. A. (1987). Al-Islami Fiy-Nijeriya wa Sheikh Usmanu Bn Fodiyo Al-Fullanniy Al-Mujahidul Islamiyl Akbar Bi-Garb Ifrƙiyya Wal-Jaddil A’ala Asshahiid Ahmad Ballo. Markazul Ta’alimul Arbiy Al-Islamiy, Agege-Nijeriya.

Boahen A. (1965). Topics in West African History. Printed in Malaysia.

Gumi A. M. (Babu Shekarar Bugu). Alƙur’ani Mai Girma da Kuma Tarjamar Ma’anoninsa Zuwa ga Harshen Hausa. Alƙur’ani da aka buga a Madina garin Manzo, wuri da aka tanada musamman na Sarki Fahad don buga Alƙur’ani Mai Girma. Madina.

Wazirin Kano A. A. (1978). Kano ta Dabo Cigari. Northern Nigerian Publishing Company Limited. Zaria, Kaduna-Najeriya.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub